Hukumar ‘yan sanda a jihar Yobe ta hana yin amfani da bakin gilashi a motoci ko kuma boyewa da kulle lambar motar.
Hukumar tace tayi hakan ne don a samu ragin masu aikata miyagun ayyuka a fadin jihar domin suna boye kansu ne don kar a gane su a kama su.
Saboda haka mai magana da yawun hukumar ta jihar, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyanawa manema labarai na DailyPost wannan labarin a ranar litinin a babban birnin jihar, Damaturu.