Hukumar yan sanda ta kama daya daga cikin barayin da suka shiga masaukin dalibai yin sata a jihar Ogun.
DSP Abinbola Oyeyemi ya bayyana cewa sunyi nasaarar kama barawon ne mai suna Sadiq Yahaya sakamakon raunin da suka ji masa inda suke musayar wuta.
Yayin sauran barayin guda biyar suka tsere da raunika a jikkunansu suka afka cikin daji.