fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta kama babban dan jarida a jihar Zamfara taki bayar da belinsa

Hukumar ‘yan sanda ta kama dan jaridar Leadership a jihar Zamfara Umaru Muradun a ranar asabar ba tare da fadin laifin daya aikata ba.

Mai magana da yawun hukumar jihar Ayuba Elkanah ne ya tabbatar da cewa sun kama shi yayin da shugaban ‘yan jaridar jihar, Ibrahim Maizare ya kira shi a waya.

Kuma hukumar ‘yan sandan ta kama shine da safiyar ranar asabar a gidan dake mahaifar gwamna Matawalle wato karamar hukumar Maradun,

Inda ta mika shi wurin hukumar CID dake babban birnin jihar wato Gusau kuma shugaban ‘yan jaridar ya jagoranci ma’aikatanss sunje neman belinsa amma hukumar taki bayar da belin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.