Hukumar yan sanda tayi nasarar kama barayi guda hudu da ake zargi da aikata lafukan sata a jihar Bayelsa.
Inda mai magana da yauwun yan sandan SP Asinim Butswat ya bayyana cewa sunyi nasarar kama su ne a mabuyarsu dake cikin birnin garin a Yenegoa.
Sannan kuma sun kwace makaman dake hannun su, yayin da ake zargin su da aikata laifukan sata da dama a cikin garin.