fbpx
Friday, July 1
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta kama kasurgumin barayon mota da makullai 29 da lambobin mota a jihar Kano

Hukunar ‘yan sanda tayi nasarar kama kasurgumin barawon mota a jihar Kano dan shekara 34 Usaman Ibrahim.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da wannan rahoton, inda yace sun kama shi a kusa da jami’ar BUK da wata farar Hillux.

Yace masu a layin Madobi ya sato motar a karamar hukumar kumbotso, kuma sun kwace makullai 29 da kambobi mota guda 9 a hannun shi.

Mai magana dayawun ‘yan sandan yayi kira ga al’umma da su riga kura sosai da dukiyoyinsu, kuma duk wani mai cigiyar motarsa ya garzaya ofishinsu na Bompai ko kuma ya kira lambar waya kamar haka 08105359575.

Leave a Reply

Your email address will not be published.