Hukumar ‘yan sanda ta kama wasu mata guda biyu kan sayar da jinjiri dan mako gida a duniya a Agege dake jihar Legas.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda na jihar Ogen ne ya bayyana hakan inda yace an kama matar ta farko ne a Sango Ota dake jihar.
Kafin ta kaisu wurin wadda ta sayar da yaron a farashin 500,000 wadda itama hukumar tayi nasarar damketa.
Sai dai fa tace da amincewar mahaifiyar jinjirin aka sayar da shi amma hukumar tayi iya bakin kokarinta don memo mahaifoyar sai dai abin ya citira.
Saboda haka ta kaisu wurin hukumar CID domin ta cigaba da bincike akan lamarin.