Hukumar ‘yan sanda a jihar Niger tayi nasarar damkw wasu masu garkuwa da mutane guda biyu da suka kashe wani yaro dan shekara 13 bayan sunyi garkuwa dashi.
Mai magana da yawun hukumar, DSP Abiodun Wasiu ne ya bayyana hakan, inda yace sunyi grkuwa dashi ne a ranar 29 ga watan Yuli.
Kuma mutanen da ake zargi guda biyu ne, wato Naifiu Umar dan shekara 18 dai Usman Sabiu dan shekara 22 sannan dukkansu su amsa laifin da ake tuhumar dasu da aikatawa.
Inda suka ce sun kashe yaron ne Yasir Salisu bayan daya manta da lambar wayar babansa, sannan kuma duk ya gane su saboda makwabtane.