Hukumar ‘yan sanda a jihar Katsina ta girmama jami’inta, Nura Mande bayan ya tsinci dala 800 a sansanin alhazai kuna mayarwa mai kudin abinsa.
Ind mai magana da yawun hukuma na jihar, Gambo Isah ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda Isa Dabban ya bashi kyautar naira 30,000 tare da shaidar girmamawa.
Jami’in ya kasance daya daga cikin ‘yan sanda dake aiki a sansanin alhazai na jihar.
Kuma ya bayyana cewa tsoron Allah ne yasa shi ya mayar da kudin wurin mai shi, Hadiza Usman.