fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta kori wani jami’inta daga aiki bayan daya lallasa wani mutun da adda

Hukumar ‘yan sandan Nakeriya kori wani jami’inta kopur Okoi Liyomo, wanda ya lallasa wani mutun da adda a jihar Rivers makon daya gabata.

Bideyon wannan jami’in ya jawo hankulan al’ummar Najeriya sosai inda har wasu ke cewa ya kamata a hukunta shi musamman matasa.

Kuma insfeto janar na ‘yan sanda ya gana da shi a babban birnin tarayya kafin a kore shi, inda kuma ya bayar da umurni a damke sa.

Yayin da hukumar ta kara da cewa ba zata laminci cin zarafin wani ko kuma aikin banza daga wurin ko wane jami’inta ba ba tare data hukuntasa ba kamar yadda take yiwa kowa.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.