fbpx
Monday, August 15
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta kwato makaman wasu ‘yan bindiga da suka tsere a jihar Legas

Hukumar ‘yan sanda ta musamman ta RRS ta kwato makaman wasu ‘yan bindiga da suka kaiwa hari suka tsere a jihar Legas.

Hukumar ‘yan sandan ta kai masu harin ne da misalin karfe biyu na dare bayan ta samu labari cewa suna labewa a yankin na Orile-Iganmu,

Kwamandan hukumar ta RRS ne ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace ‘yan bindigar sun yadda makaman nasu sun tsere yayin da suka ga hukumar na tunkaro su.

Kuma yace sun dauke bindugun nasu guda biyu kuma suna gudanar da bincike akan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.