fbpx
Friday, August 12
Shadow

Hukumar ‘yan sanda ta mamaye babban birnin tarayya Abuja biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka ce zasu kai kwanan nan

Infeto janar na ‘yan sanda, Alkali Usman Bana ya bayar da umurni a kara yawan hukumar tasu a babban birnin tarayya Abuja don kare rayuka al’umma da kuma dukiyoyinsu.

A yau ranar talata shugban ‘yan sanda ya bayyana hakan a wasikar data fito daga hannun mai magana da yawun hukumar ta kasa, CSP Olumuyiwa Adejobi.

Inda yace ya bayar da wannan umurnin ne biyo bayan barazanar da ‘yan bindiga sukayi na cewa zasu kai hari Abuja kwanan nan.

A karshe yayi kira ga al’ummar kasar nan dama ‘yan jarida bakidaya cewa su daina yada labaran bogi akan ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published.