Hukumar ‘yan sanda tayi nasarar cafke shugaban kungiyar ‘yan ta’addan da suka hana mutanen kauyen Tungar Dutsi gudanar da bukin Sallah cikin limana a jihar Zamfara.
Mai magana da yawun ‘yan sandan, Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan inda yace sun kama shugaban nasu Bala Minista.
Yace a ranar uku ga watan mayu ne mutanen kauyen suka sanar dasu cewa wasu mutane da bundugun baushe da adduna da wukake sun mamaya kauyen.
Kuma yanzu suna tsare da shugaban nasu yayin da suke shirin hukunta shi akan laifin daya aikata.