A ranar asabar hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama dan jaridar Leadership, Umaru Maradun ba tare da fadin laifinsa ba.
Wanda hakan yasa shugaban kungiyar ‘yan jaridar jihar Maizare ya kira mai magana da yawun hukumar, Ayuba kuma ya tabbatar da cewa sun kama shi sun kai shi wurin hukumarsu ta CID.
‘Yan jaridar sunje sun bukaci belinsa daga farko amma hukumar taki bayarwa, sai dai yanzu daga bisani ta amince ta bayar.