fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Hukumar ‘yan sandan kasar Tamzania ta sako shahararren mawakin Najeriya Kizz Daniel bayan ta kama shi

Hukumar ‘yan sandan kasar Tanzania ta sako shahararren mawakin Najeriya Oluwatobiloba Daniel, wanda aka fi aani da Kizz Daniel.

Humumar ta sako shi ne bayan ta kama shi saboda yaki zuwa yayi wasa a wani gidan taro da suka biya shi kudi a daren ranar lahadi.

Wanda hakan yasa suka kama shi, amma kungiyar ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen waje sun ce an sako sa a yammacin yau.

Inda suka kara da cewa wakilansa zasu gana da hukumar ‘yan sandan kafin ya dawo gida Najeriya gobe.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.