Hukumar ‘yansanda ta baiwa ‘yan Najariya shawarar kulle layukansu ta hanyar amfani da lambobin sirri.
Kakakin ‘yansandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka.
Yace an gano wasu barayi dake satar sim su kwashewa mutum duka kudin dake akawun dinsa na banki.
Yace wanda kawai basa iya kwashewa kudi shine wanda ya kulle layin wayarsa da lambobin sirri.
Dan hakane suke baiwa mutane shawarar daukar wannan mataki.