fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Hukumar ‘yansanda zata kori jami’an SARS 37 daga aiki

Hukumar kula da aikin dan sanda ta kasa, PSC ta tsame sunayen ‘yansanda 37 dake aiki a rundunar SARS dan sallamarsu daga aiki saboda samunsu da laifuka.

 

Hakanan an ware sunayen wasu 24 da suma za’a hukuntasu saboda aikata wasu laifuka da basu kai na kora daga aiki ba.

 

Wannan na kunshene cikin rahoton da kwamitin shugaban kasa na binciken ayyukan kungiyar ya bayar. Rahoton wanda shugaban PSC, Musiliu Smith da kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa, Tony Ojukwu suka gabatar sun bukaci a gaggauta yin amfani da shawarwarin da ya bayar na ko dai a canjawa Rundunar Fasali ko kuma a canjata gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.