Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta gabatar da takardun shaidar cin zabe ga zababbun shugabannin kananan hukumonin jihar kano.
A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na KANSIEC, Dahiru Lawan Kofar Wambai, wanda aka rabawa manema labarai, Shugaban Hukumar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka, ya ce biyo bayan nasarorin da zababbun jami’ain suka samu a zaben da aka gudanar hukumar taga da cewar rarraba musu shaidar cin zabukan nasu.