Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta gargadi jam’iyyun kasa Najeriya cewa ba zata kara masu wa’adin data sa na ranar 15 ga watan Yuli ba don gabatar mata da ‘yan takarar gwamna da kuma majalissar jiha ba.
Kwamishinan hukumar ta fannin yada labarai ne ya bayyana hakan ranar alhamis, watau Fetus Okoye.
Amma yace za’a cigaba da yiwa mutane rigistar katin zabe har sai lokacin da hukumar zaben ta bayyana nasu wa’adin.