fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Hukumar zabe ta INEC tace da yiyuwar mutanen dake gida Kurkuku su kada kuru’unsu a zaben shekarar 2023

Hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa sa yiyuwar mutanen kasar dake gidan Kurkuku su samu damar kada kuru’unsu a zabe mai zuwa ma shekarar 2023.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan bayan ya karbi bakunci shugaba Kurkukun Najeriya wato Haliru Nababa jiya ranar talata kan wannan batun.

Akalla akwai mutane 73,726 ne a gidajen Kurkuku kasa Najeriya a shekarar 2020.

Kuma shugaban hukumar yace da yiyuwar a barsu su kada kuru’un nasu daga gidajen yarin kamar yadda ake yi a Kenya da kuma Afrika ta Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.