Jam’iyyar mulki ta APC ta karyata rahotannin dake bayyana cewa ta tanadi naira triliyan 6.5 don tayi magudin zabe a shekarar 2023.
Wannan labarin nata yawo a kafafen sada zumunta da rahotanni a kwanakin nan, amma yanzu jam’iyyar ta bayyanawa hukumar zabe ta INEC cewa abokan adawa suke wallafa labarin.
Inda wani rahoto ya bayyana kudin da APC ta tanada don sayen kuru’u da jami’an tsaro dama hukumar zabe bakidaya ya kai kusan rabin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2022.
Amma mai magana da yawun jam’iyyar APC, Felix Morka ya bayyana cewa wannan labaran kanzan kurege ne kuma abokan adawa ne suke yada shi.