fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hukumar Zabe ta sanya ranar 6 ga Nuwamba a matsayin ranar zaben gwamna a jihar Anambra

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta sanya ranar 6 ga Nuwamba, 2021, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra.

Sanarwar na kunshe ne ta cikin jawabin da Shugaban masu wayar da kan masu zabe Festus Okoye ya fitar.

Hukumar zaben ta bukaci jam’iyyun siyasa dasu gudanar da zabukan fidda gwani akan ka’ida batare da son rai ba.

Hakanan hukumar ta fitar da Jaddawalin zabukan fidda gwani inda ta sanya ranar 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a gudanar da babban zaben gwamnan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.