Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa hukumar zata tsawaita lokaci don a cigaba da yin rigistar katin zabe.
A ranar 30 ga watan yuni ne hukumar tace zata daina yin rigistar, amma yanzu tace zata kara lokacin bayan kungiyoyi da dama sun bukaci hakan kamar SERAP da sauran su.
A ranar juma’a ne ya bayyana hakan a babban birnin tarayya Abuja, kuma yace zasu fara ba mutne katin zaben a watan oktoba.
Sai dai ba fadi tsawon lokacin da suka kara ba.