Hukumomi sun shawarci ƴan Afirika ta kudu su riƙa wankan minti biyu

Hukumomin samar da ruwa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, sun bukaci mazauna birnin da kewayen da su taƙaita yawan ruwan da suke amfani da shi sakamakon karancin ruwa da ake fama da shi wanda zai iya haifar da durƙushewar al’amura.
Kamfanonin samar da ruwa na ‘Rand’ da ‘Johannesburg’ a ranar Lahadin da ta gabata sun ce yawan ruwan da mazauna yankin ke amfani da shi “yana kawo cikas ga tsarin samar da ruwa” kuma ya haifar da ƙarancinsa a rumbun adana ruwan.
Kamfanonin sun buƙaci mazauna yankin da su taƙaita wanka zuwa mintuna biyu bayan haka, kada su yi amfani da ruwa sai idan sun yi ba-haya, kuma su kiyayi wanke motoci har sai karshen mako-mako, su guji amfani da ruwa mai tsafta ga lambuna, da kuma bayar da rahoton duk inda ruwa ke tsiyaya.
A halin yanzu Johannesburg na ƙarƙashin takunkumin ruwa na shekara-shekara, yawanci daga Satumba zuwa Maris.
Rashin ruwa na baya-bayan nan ya haifar da rashin gamsuwa a tsakanin mazauna da cibiyoyi, kamar asibitoci.