fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hukumomin kwallan kafar turai a yau zata gudanar da wani taro

An dakatar da gaba daya manyan gasannin lig na kwallon kafa a kasashen nahiyar Turai a makon da ya gabata, a wani al’amari da ya jefa wasan kwallon kafa a cikin wani kalubalen da bai taba fuskanta ba a wannan zamani, kuma bisa ga dukkan alamu, dole ne ma a dau mataki a kan gasannin zakarun nahiyar Turai, wato Champions League da Europa League.

Hukumar kwallon kafar Turai a yau Talata za ta gudanar da wani taro na wakilai 55 na hukumomin kwallon kafa na kasashe da kungiyoyi, sannan daga bisani ta gudanar da taron majalisar zartaswarta a shelkwatarta da ke Switzerland.

Karanta wannan  Ronaldo ya cewa Manchester ba zai halacci atisayi yau ba bayan data cigaba da ce masa ba zata sayar dashi ba

Nahiyar Turai ta kasance tamkar cibiyar wannan annoba ta coronavirus, inda yanzu haka hukumomi suka garkame kofofi a Italiya da Spain, yayin da Faransa ke biye, haka kuma sauran kasashe a nahiyar suke garkame iyakoki don dakile yaduwar wannan cuta.

Fiye da mutane dubu 2 da dari 1 ne suka mutu a Italiya, kasar da za ta karbi bakoncin wasan farko na wannan gasa ta Euro 2020.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.