Daga Abubakar A Adam Babankyauta
A karon farko shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa hukumomin tattara bayanan sirrin Nijeriya sun bashi kunya.
Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa shugaban NMuhammadu Buhari ya bayyana cewa hukumomin tattara bayanan sirri na ƙasar sun ba shi kunya bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da ya kai gidan yarin a ranar Laraba, kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
Hukumomin tattara bayanan sirrin Nijeriya sun ba ni kunya. Ta yaya ƴan ta’adda za su shirya, su ɗauki makamai su kai hari ga wurin da jami’an tsaro suke kuma su gudu?
Shugaban ya shafe kusan minti 30 a gidan yarin kuma ya yi tambayoyi da dama.
Daga cikin tambayoyin da shugaba Buhari ya yi sune kamar haka.Ta yaya jami’an tsaron da ke gidan yarin suka gaza daƙile harin? Fursunoni nawa ne a ciki? Guda nawa ne za a iya bayar da bayaninsu? Jami’ai nawa ne ke aiki lokacin da lamarin ya faru? Nawa ne ke ɗauke da makami?
“Masu gadin gidan yarin sun hau kan hasumiya? Shin kemarar tsaro tana aiki?” Duka waɗannan tambayoyin shugaban ya yi su a gidan yarin.
Bayan haka shugaban ya ce yana buƙatar a kai masa cikakken bayani kan yadda wannan lamarin ya faru.
Mudai muna rokon ubangiji Allah ya azurta kasar mu Nijeriya da zaman lafiya mai daurewa.