Hukumar ‘yan sanda a jihar kebbi ta damke Abubakar Isma’il, manajan centre na rubuta jarabawar shiga jami’a ta Jamb kan satar kwamfutoci.
Hukumar ta kama shine a karamar hukumar Zuru da zargin sace kwamfutocin na HP Laptop guda 83 kuma ya sayar dasu akan naira 40000 duk guda daya.
Dr Michael Ezra Dikki ne ya kai karan shi wurin hukumar ‘yan sandan kuma sunyi nasarar kwato wasu komfutocin guda 76 a hannunsa.
A halin yanzu dai hukumar na cigana da gudanar da bincike kafin ta maka shi a kotu domin a yanke masa hukunci.