fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Idan aka sake aka kara kudin man fetur sai mun tsayar da al’amura cak a Najeriya>>Inji matasan Naija Delta

Kungiyar faftutuka ta Naija Delta sun bayyana cewa idan aka sake aka kara kudin man fetur to zasu tsayar da al’amura cak a Najeriya.

 

Gwamnatin tarayya dai ta bayyana cewa a cikin shekarar nan ta 2022 da mukene zata cire tallafin man fetur din.

 

Lamarin dai zai sa farashin man ya tashi sama sosai dan za’a rika amfani da farashin kasuwar Duniya ne.

 

Saidai hakan bai yiwa yawancin ‘yan Najeriya dadi ba inda da yawa suka yi watsi da wannan shirin.

 

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba

Gwamnatin dai tace wasu manya ne kawai ke amfana da tallafin man ba wai ainahin talakawa ba, inda tace zata gano talakawa mafiya talauci akalla Miliyan 40 ta rika basu tallafin Naira Dubu 5 duk wata.

 

Shugaban Kungiyar dake ikirarin fafutukar neman ‘yanci a Naija Delta, Israel Joe ne ya bayyana haka, yace zasu tsayar da al’amura cak a kasarnan idan aka kara kudin man fetur din.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.