Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan aka zabeshi shugaban kasa, idan ya tashi sauka, matashi zai baiwa.
Yace zai tabbatar ya horas da matasan da zasu karbi mulkin kasar sannan ya mika musu mulkin.
Yace yana son yin aiki tare da matasa saboda suna da kwazo da kuma hazaka akan abubuwan ci gaba.
Ya bayyana hakane yayin da wata kungiyar magoya bayansa suka kai masa ziyara.