fbpx
Friday, February 26
Shadow

Idan ba’a saurari koken Mutane ba aka dauki mataki, Abubuwa zasu kara tabarbarewa>>Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III

Me Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa idan ba’a dauki matakin sauraren koken mutane ba aka dauki matakin da ya dace, abubuwa zasu kara tabarbarewa.

 

Sarkin Musulmi ya bayyana hakane a wajan taron tunawa da nadin sarautar Oni of Ife karo na 5, Oba Adeyeye Ogunwusi wanda aka yi jiya, Juma’a a Ibadan.

 

Ya bayyana cewa taruwar sarakunan gargajiya daga kowane bangare na kasarnan a guri daya, Abin Alfaharine, musamman a irin wannan lokaci da wasu ke ta kiran a raba kasar.

 

Ya kuma nanata maganarsa ta matsalar tsaro a Arewa inda yace duk da shi ba dan siyasa bane amma uban ‘yan siyasa ne, dan haka zai yi magana akan Siyasa, yace idan ka duba shafukan jaridu, da yawa sun dauki labarin maganar da yayi kan matsalat tsaron Arewa a Abuja.

 

Yace dan haka wannan alamace dake nuna sakon na kaiwa kunnen wanda ya kamata. Yace idan mutane suka yi koke akan wani abu, ya kamata a dauki mataki, domin idan ba’a dauki mataki ba, lamura zasu tabarbare sannan kuma idan lamura suka tabarbare Allah ne kawai zai iya maganinsu, dan haka bai kamata a bari akai wancan mataki ba.

“If you check the newspapers today (yesterday), almost all of them have this very bold headlines on what I said on Thursday. It means some people are watching; they are listening, they are reading.

“What we want is for them to implement, act. If you listen, you will hear what people have been saying and crying for. When you don’t act, then things will get worse. When things get worse, they will get worst. When they get worst, of course, it is only Almighty Allah who will come and help us.

 

“So, let’s not allow that; let’s rise up and make things change in this great country. Almighty couldn’t have made a mistake when He put this country together. And if He wants to do whatever He wants to do, He will just do it. He will separate this country, divide it into one million little pieces and you will need visa to go somewhere and you may not get the visa.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *