DAGA Aliyu Ahmad
Wata matashiya mai suna Fati Gombe ta bayyana cewa idan ba ta samu damar auren tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ba, za ta iya samun matsala a rayuwarta.
Fati wadda ‘yar asalin jihar Gombe ce, ta shaidawa RARIYA cewa kada jama’a su yi zaton tana son Janar Babangida saboda abin duniya, a’a tana kaunar sa ne saboda Allah. Kuma ta amince za ta zauna da shi har tsawon rayuwar ta idan Allah ya kaddara ta aure shi.
Cikin hawaye tare da nuna shaukin soyayya ga Janar Babangida a cikin wasu bidiyoyi da ta turowa RARIYA, Fati ta kara da cewa ta jima tana kaunar tsohon shugaban kasan ba don komai ba sai don Allah. Don haka ta yi fatan Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri Janar Babangida.