fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Idan da ranka zaka kasha kallo wata kyanwa yar asalin kasar Belgium ta kamu da cutar Numfashi wanda aka fi sani da Coronavirus

Ita dai wannan kyanwa yar asalin kasar Belgium ta kamu da cutar Numfashi wanda aka fi sani da Coronavirus.

Kyanwar dai ba’a bayyana shekaraun ta ba, sai dai kamar yadda majiyar Brussels Times reported ta rawaito tace, wannnan kyanwa ta kamu da iftila’in annobar cutar ne daga gun mai ita Wanda aka rawaito yana dauke da cutar kamar yadda majiyar ta shaida.

Bayan gwajin da akai wa kyanwar an tabbatar itama ta kamu da cutar bisa ga wasu alamomi da suka fara bayyana a jikin ta, inda aka samu tana yawan amai gami da yawan gudawa babu kakkautawa a cewar wani kwararran likita mai suna Steven Van Gucht wanda mai bincike ne a asbitin Jami’ar Ghent University’s a fannin magun-guna.

A cewarsa ya duwar cuta tsakanin mutum da kuma dabbobi abu ne mai saukin gaske.

Sai dai harzuwa yanzu baya ga wannan kyanwa babu wani rahoto da aka samu game da an sake samun wata mage data kamu da wannan cuta, baya ga wani kare da shima aka samu dauke da cutar Covid-19.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.