fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Idan dai da gaske kun kashe Shuwagabannin ‘yan Bindiga a Zamfara, ku nuna mana gawarwakinsu>>Sheikh Gumi ga sojoji

Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr Ahmad Gumi ya bayyana cewa, idan da gaske sojojin Najeriya sun kashe shugaban ‘yan ta’adda to su nunawa mutane shaida.

 

Gumi ya kuma kara jaddada matakinsa na cewa, abinda ya kamata a yi dan kawo karshen wannan matsalar itace sulhu.

 

Kakakin malam, Tukur Mamu ne ya bayyanawa manema labarai haka a ganawa dasu, yace yawancin hare-haren da sojojin ke kaiwa ana kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.

 

Yace a misali a ziyarar da ya kaiwa ‘yan Bindigar jihar Naija, sun nuna masa wani kauye da basu da alaka dasu da sojojin sukawa ruwan bamabamai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.