Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi jira ga ‘yan Najariya da su zabi Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda zai gajeshi idan suna son ganin ci gaban ayyukan da yake.
Shugaban ya kara da cewa, zasu yi dukkan mai yiyuwa wajan ganin an jawo hankalin ‘yan Najariya sun zabi APC a 2023.
Hakan na kunshene a cikin sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar inda yace shugaban ya bayyana hakane yayin karbar bakuncin mutane daga jihar Nasarawa.
Yace jihar ta Nasarawa na da rawar da zata taka wajan ganin jam’iyyar su ta yi nasara a zaben shekarar 2023 me zuwa.