Kungiyar dake ikirarin kafa kasar Biafra ta MASSOB ta gargadi gwamnatin tarayya da cewa, kada a bar Nnamdi Kanu ya mutu a hannun DSS.
Shugaban kungiyar, Uchenna Madu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace kamata yayi a bar likitan Nnamdi Kanu ya dubashi.
Yace idan Kanu ya mutu a hannun gwamnati za’a gwabza yakin da gwamnatin ba zata iya shawo kanshi ba.