fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Idan gwamna Umahi ya zama shugaban kasa, Najeriya ba zata yi sati biyu ba zata ruguje>>Inji Mutanen jihar sa ta Ebonyi

Gwamnan jihar Ebonyi,  David Umahi ya bi sahun jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya je ya gayawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa, zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

 

Saidai tun kamin a je ko ina, Gwamnan ya fara samun tangarda daga cikin gida.

 

An samu wata kungiya ta ‘yan Asalin jihar ta Ebonyi, (AESID) sun fito suna cewa kada a zabeshi.

 

Kungiyar tace idan aka sake aka zabi Gwamna Umahi lallai Najeriya ba zata kai labari ba. Sunce da wuya kasar zata kai sati daya idan Gwamna Umahi ya zama shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.