Dan majalisa daga jihar Filato, Yusuf Gadgi ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar ta bar mutane su dauki makamai dan kare kansu.
Ya bayyana cewa ta hakane za’a iya kawo karshen matsalar tsaron dake damun kasarnan.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN yace Yusuf ya bayyana hakane a jiharsa ta Filato.
Ya kuma yi kira ga majalisa data yi dokar da zata baiwa ‘yan Najeriya damar rike makamai dan kariyar kai.
Yace misali wanda suka kawowa garinsa hari, idan suka san mutane na da makamai ba zasu kawo harin ba, idan ma su kawo, to yawan mutanen da suka mutu da ba zai kai haka ba.