Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya shiga tattaunawa ta yanar gizo kan wakilan jam’iyyun siyasa da ke neman kudi kafin zaben kowane dan takara.
A cikin wani sakon twitter, ya bayyana cewa idan delegates sun canacanci a biya, ba kamata a dinga zagin talakawa da ke neman buhunan shinkafa kafin su yi zabe ba.
Sani ya kuma bayyana cewa wasu ’yan takarar da suka yi rashin nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka kammala kwanan nan, suna ta bi gida-gida suna kama wakilan da suka karbi kudadensu ba su zabe su ba.
Karanta wannan Hukumar NAFDAC ta haramta yin amfani da wani man kai da ake sarrafawa a Nahiyar Turai