Ministan harkar jiragen sama na farko a Najeriya, Chief Mbazulike Amaechi ya bayyana cewa dan takarar Labour Party Peter Obi ne yafi kowa cancantar zama shugaban kasa.
Inda yace Peter Obi ne kadai gwamnan da yayi mulkinsa ya kare ba tare da hukuma ta ne shi kan satar ko sisi ba, domin shi bai ma san ofishin EFCC da ICPC ba.
Saboda haka idan har bai ci zabe ba to tabbas dama Allah yayi cewa Najeriya zata sha bakar wahala kuma zata shiga matsanancin hali.
Tsohon ministan dan shekara 93 ya bayyana hakan ne a gidansa a karshen makon nan yayin dayake ganawa da manema labarai.