fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Idan Har Za A Kashe Almajiranci To Shi Ma Karatun Boko A Kashe Shi>>Sheik Aliyu Adarawa

Babban malamin addinin musulunci a Nijeriya kuma shugaban majalisar malammai na Jihar Neja, Sheik Aliyu Muhammad Sani Adarawa ya bayyana takaicin sa akan yadda gwamnati da wasu gwamnoni suka fi maida hankali akan kashe almajiranci maimakon zamanantar da tsarin karatun.

 

 

Malamin ya bayyana hakanne a lokacin da yake rufe tafsirin da yake gabatarwa a garin Kontagora dake Jihar Neja a yau laraba, Sheik Adarawa ya ce ” Kashe tsarin almajiranci da gwamnati ke ƙoƙarin yi ba adalci bane, domin suma almajirai ƴan ƙasa ne kamar kowa suna da ƴancin zuwa duk garin da suke so domin neman ilimi kamar yadda kowani ɗan Najeria keda shi.

 

Sheik Aliyu adawarawa ya ƙara da cewar “Idan har za’a bar ƴan boko suje wasu sassan Najeria harda ƙasashen waje neman ilimi kuma karatun kwana ne domin shima almajiranci ne, to babu dalilin da zai sa a hana wasu rukunin mutane zuwa almajiranci domin neman ilimi na addinin musulunci dan haka suma almajirai dole ne a barsu suje duk garin da suke so su nemi ilimi domin suna da ƴanci a addinance da kuma dokar ƙasa, idan kuma za’a kashe almajiranci to shima tsarin boko a kashe shi ko wani yaro ya zauna garin su yayi firamare da sakandare da jami’a na jeka ka dawo.

 

 

Idan har ana tunanin sanadiyyar zuwa almajiranci shike sa wasu yara su lalace wanda wasu ke tunanin in sun girma zasu zama matsala a ƙasa, yara nawa ne suka lalace sanadiyyar karatun boko wasu ma gaban iyayen su suka lalace, amma duk wannan ba abun la’akari tare da nazari dan ɗaukar mataki bane sai almajirai.

Karanta wannan  Alkali ya kashe auren wani mutum sannan ya aure matar daga baya

 

 

Ga manyan matsalolin da suka addabi al’umma amma ba’a maida hankali a kan su ba sai zancen kashe almajiranci-Inji shi.

 

 

Yadda gwamnati ta fitar da tsari akan karatun boko haka yakamata ta fitar da tsari akan almajiranci, gwamnati na kashe kuɗaɗe akan karatun boko suma almajirai nada ƴancin a ware masu wasu kuɗaɗe da za’a riƙa kula da karatun su, idan ma gwamnati zata samar da tsarin duk mahaifin da zai tura ɗan sa karatu ya tanadar masu ɗan abunda zaici hakan nada kyau.

 

 

Aƙarshe Sheik Adarawa ya shawarci gwamnati inda yace ” maimakon kashe almajiranci kamata yayi gwamnati ta ɗora daga tsarin da waccan tsohuwar gwamnati ta fara na makarantun tsangaya domin hakan zai taimaka wurin zamanantar da tsarin karatun, bamu goyon bayan bara domin haramun ne a addinance Amma almajiranci kan halas ne dan haka bamu goyon bayan kashe almajiranci, gwamnati ta canja tunani a wannan mataki da take ƙoƙarin ɗauka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.