Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce zai yi tunanin ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023 ne kawai idan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nuna sha’awar tsayawa takarar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Television’s Sunday Politics, inda ya bayyana cewa matsayarsa ta dogara ne kan mutunta Jonathan da ya nada shi ministan babban birnin tarayya (FCT) a shekarar 2010.
Gwamna Bala Muhammad ya bayyana cewa: “Jonathan yana daya daga cikin wadanda yake girmamawa a kasar nan.