Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kalubalanci Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ya je a yi hira dashi ta awa daya a gidan talabijin.
Atiku yace yin hakan zai sa ‘yan Najariya su fahimci lafiya da kuma kaifin basirar Tinubu.
Atiku yayi wannan maganane a matsayin raddi ga cewar da kungiyar yakin neman zaben Tinubu ta masa cewa makaryacineshi.