fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Idan Ka Sake Shigowa Maiduguri Sai Na Kai Maka Hari, Barazanar Shekau Ga Buhari

Shugaban ‘yan ta’addar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kada ya sake ya kara shiga jihar Borno.

Shekau ya bayyana hakan ne a wani sabon bidiyo da ya saki awanni kadan bayan shugaban kasar ya kai ziyara birnin na Maiduguri, domin yayi musu jaje akan harin da aka kai Auno.
Shekau ya ce za su kai wa shugaban kasar hari matukar ya kara zuwa birnin na Maiduguri.
“Buhari ya shigo Maiduguri yana takama da shi mutumin kirkine, Kada ya kara zuwa daga yau,” Shekau ya bayyana haka a cikin harshen Hausa.
Haka kuma shugaban ‘yan ta’addar ya bayar da ka’idoji akan sauran ‘yan matan Chibok da suka rage a wajen su.
Duk da cewa an saki 100 daga cikin ‘yan mata 276 da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandare ta Chibok, dake jihar Borno, a shekarar 2014, da yawa daga cikinsu suna hannun ‘yan ta’addar.
A sabon bidiyon Shekau ya ce za su saki ‘yan matan idan har gwamnatin tarayya ta saki ‘yan kungiyarsu da ta rike a gidan kurkuku.
Wannan na zuwa ne bayan ‘yan kungiyar sun kai hari a garin na Maiduguri, jim kadan bayan fitar shugaban kasar daga garin a jiya 12 ga watan Fabrairun shekarar 2020.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Alkali zai raba auren matar dake tuhumar uwar mijinta da shan mata sigari a cikin dakinta a garin zariya


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.