fbpx
Friday, July 1
Shadow

Idan kuka zabeni shugaban kasa, Sambisa zan koma da zama kuma cikin watanni 6 zan gama da matsalar tsaro>>Manjo Al-Mustapha

Tsohon babban dogarin shugaban Najeriya na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Al-mustapha ya ce idan har ya zama shugaban kasar, a cikin wata shida zai kawo karshen matsalar tsaro ta Boko Haram da ta addabi Najeriya.

Almustapha ya ce, zai je ya tare a dajin Sambisa, da ke jihar Borno, inda nan ne ake ganin matattarar mayakan Boko Haram, tsawon sati daya domin daukar duk matakin da ya wajaba a dauka domin ganin karshen mayakan.

Ya ce idan har ya zama shugaban kasa to lalle ne abin Allah ya shimfida za a yi wa dole ne a yi shi, ya ce, ”komai zafinsa a idon ko su waye”, yana mai bayar da misali da matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

Ya nuna takaicinsa da damuwa kan yadda yake ganin sojojin Najeriya yanzu sun lalace ba su da kishi da kuzari kamar da, inda ya ce, ”Ka ga soja, duk sojan Najeriya ni ina ganinsa daidai yake da dan-sanda na da, saboda sun riga sun zama dan-sandan, kuma ‘yan-sandan da kuke da su sun gurbata, sun gurbata. Ni akwai abin da in zan yi a wata shida za ka ji tsoron abin da za a yi amma kuma shi ne gaskiya.”

Ya ce zai yi wa sojojin Najeriya garambawul a cikin wannan wa’adi na wata shida, wanda hakan abu ne da zai kasance da zafi amma kuma ya zama wajibi domin ya dawo da karfi da kuzarin sojojin Najeriya kamar yadda aka san su a baya.

”Misali ba shegantakar nan ta Boko Haram ba, wallahi ni zan ce a wata shida indai ba ta yi ba, duka manyan nan sai an rage muku girma, kuma za ku tafi gida, kuma za a hukunta ku kudin da aka ba ku sai kun fid da shi, sai an yi musu probe (bincike), a wata shida a matsayina na shugaban kasa zan je Zambiza can zan koma can zan yi hutu, zan yi hutun sati wurin in wani abu ya taba ni ma gani ” in ji shi.

Karanta wannan  Dalilin dayasa ni da Wike ba zamu goyi bayan Atiku ba duk da cewa jam'iyyar mu daya, cewar tsohon gwamnan Ekiti

Tsohon dogarin na Abacha yana magana ne a hira ta musamman da BBC, inda ya bayyana shigarsa jerin masu neman takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a shekara mai zuwa ta 2003, inda zai nemi takara a karkashin jam’iyyar Action Alliance.

Manjo Al-Mustapha wanda yake nuna takaicinsa kan irin halin da kasar ta shiga na tabarbarewar tsaro, ya ce lokaci ya yi da zai shiga siyasa gadan-gadan.

Ya ce wasu kungiyoyi ne suka hada kudi, suka sai mishi takardar neman takarar suka ce ga gumummawarsu ga kuma jam’iyyar da zai yi takara.

Dangane da kin shigarsa wata daga cikin manyan jam’iyyun kasar, sai ya nuna cewa ya yi hakan ne domin wadannan manyan su yake gain sun gurbata kasar, inda ya yi misali da cewa, Shugaba Buhari, mutum ne da suka sanshi tun suna kanana.

Ya ce, ”amma wadanda suka kewaye shi su ne gurbatattun Najeriya, suna nan da yawa.Yanzu in ka zauna ka ce ka dora wannan gwamnati a sikeli, ta’adin da suka yi ranar da zai fara fahimta, na san ranar zai sake tunani da yawa ” in ji Al-Mustaphan.

Haka kuma ya nuna sakacin gwmnatin Buhari na yadda, ya ce idan Shugaban ya danka wa mutane amana ba ya bibiya, inda ya ce shi idan ya samu shugabancin daga kansa zai nuna misali na bin doka, kuma idan ya dauki rantsuwa to ba zai sassautawa kowa ba, domin doka kamar ruwan zafi take, duk wanda ya saba doka, to doka za ta hau kansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.