Ministan kwadag,Chris Ngige ya bayyana cewa, idan aka zabeshi shugaban kasa a Najeriya za’a ga aiki da cikawa.
Ya bayyanawa magoya bayansa hakane a yayin da suka tareshi a tsakanin jihar Anambra da Enugu.
Ngige yace zai yi kokarin dorawa a aikin da yayi a matsayin minista.
Yace kuma ya gana da gwamnonin yankinsu inda suka nuna mai goyon baya kan takarar tasa.