Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yiwa kabilar Inyamurai Alkawarin cewa idan suka zabeshi ya zama shugaban kasa, zai tabbatar Inyamuri ya gajeshi.
Atiku ya bayyana hakane a jihar Enugu yayi da yake yakin neman zabe.
Yace ya dauki kabilar Inyamurai da muhimmanci, shiyasa ma ya dauko Inyamuri kuma daga kudu maso kudu ya zama mataimakinsa.