fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Idan Na fidar da wakar Buhari ‘yan Adawa sai sun rasa bakin Magana>>Rarara

Tauraron mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa idan ya fitar da wakar da yake shirin rerawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari to ‘yan Adawa Gum zasu yi.

 

Yayi wannan bayanine a karin hasken da yayi kan tara masa kudin Dubu-Dubu da zaiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari waka dasu.

Yace a daina biyewa ‘yan Jarida suna wallafa kanun Labarai masu daukar hankula ne kawai amma shi yana so ne ya nunawa ‘yan Adawa cewa har yanzu akwai masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma suma tare dashi hakanan shima yana tare dasu.

 

Rarara yace idan fa ya saki wannan waka tashi to ko ‘yan Adawa dole su saki kari dan ba zasu ce ba’a musu komai ba. Yace zai zayyano ayyukan da shugaban kasar yayi ne a wakar tasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.