Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa burinsa yanzu shine ya fara rubuce-rubuce dan ya samu Giri na digirgir watau,PhD.
Yace sannan kuma zai ci gaba da bincike da rubuce-rubuce har ya zama farfesa saboda yana son komawa tsohuwar sana’arsa ta koyarwa a jami’a amma a wannan karin a kasashen turai.
Sarkin ya bayyana hakane a hirar da Arise TV ta yi dashi inda yaci gana da cewa idan ya zama Farfesa da wuya a samu mutum kamarsa, wanda ya taba zama shugaban bankin kasuwanci sannan ya zama gwamnan babban bankin Najeriya sannan ya zama sarki sannan kuma Farfesa. Yace da wannan nasarori babu jami’ar Duniya ko Harvard ko ma wacce da ba zata daukeshi aiki ba.
A jiya dai Tuni Me martaba har ya isa kasar Ingila inda ake sa ran zai fara aiki dan cimma wannan buri nasa.