fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Idan Na Zama Shugaban Kasa Insha Allahu Zan Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Kaduna Da Sauran Jihohin Arewacin Nijeriya Da Kasar Baki Ɗaya– Saraki

Dan takarar shugaban kasa, Bukola Saraki ya yi alkawarin yaki da rashin tsaro idan aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.

Wani dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Dakta Bukola Saraki, ya ce zai kawo karshen rashin tsaro a Kaduna idan ya zama shugaban kasar Najeriya.

Dakta Saraki ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ya gana da wakilan jam’iyyar PDP da kuma shugabannin jam’iyyar a jihar Kaduna.

A wajen taron, tsohon shugaban majalisar dattawan ya jaddada cewa idan babu tsaro, al’umma ba za su iya ci gaba ba.

“Wannan ne ya sa lokacin da na gana da Wakilai da Shugabannin Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna a ranar Lahadi, na yi alkawarin cewa tare da goyon bayansu, idan na zama Shugaban Najeriya na gaba, zan kawo karshen matsalar rashin tsaro a Kaduna, da fadin Arewa maso Yamma, da ma kowa da kowa.” in ji Saraki.

Ya kara da cewa, “Da zarar mutane na iya tuka mota cikin aminci, su tashi a jirgin sama, su hau jirgin kasa daga Kaduna zuwa wasu jihohi. A yau, da rashin tsaro yayi kawanya a Kaduna, zuwa da dawowar jihar ya zama mai hadari da ban tsoro.

Karanta wannan  An shiga rudani bayan da fadar shugaban kasa ta caccaki kungiyar dattawan Arewa ba tare da kungiyar tace komai ba

“Saboda haka, zan tabbatar da cewa mun tura sabbin kayan aiki, na zamani da fasaha don kawo karshen ‘yan fashi da ta’addanci a fadin kasar.”

A wajen Dokta Saraki, tsaro shine babban abin da ya fi mayar da hankali a yakin neman zabensa na shugaban kasa. A baya-bayan nan ne dai tsohon dan majalisar ya yi Allah wadai da yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da harkokin tsaro a kasar.

A cewarsa, rashin iya daukar nauyin kowa ne ke da alhakin ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a kasar.

Ya nanata cewa a halin yanzu al’ummar kasar ba su da wani abin jin dadi na tura kowa zuwa Villa, don haka sai wanda ya kware kamar shi ya cancanci ya karbi ragamar mulki a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.