Dan takarar neman shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC, Orzu Kalu ya bayyana cewa, idan ya zama shugaban kasa, zai mayar da Najeriya tana gasa da kasar Japan wajan ci gaba.
Kalu ya bayyana cewa babu wanda yafi cancantar zama shugaban kasa kamarshi saboda a yanzu haka akwai ‘yan Najeriya 13,000 dake cin abinci a karkashinsa.
Ya bayyanawa manema labarai cewa cikin shekaru 4 zai farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Yace zai karfafa tattalin arzikin Najeriya ya rika gasa dana kasashen Amurka da Japan.
Yace duk me neman takarar shugabancin Najeriya ya kamata yana iya sanya mutane farin ciki kuma zai iya magance matsalar tsaro.