Dan takarar gwamna na jam’iyyar NYPT a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Tanko Yakasai ya bayyana cewa sai idan Tinubu ya dakko mataimaki musulmi daga Arewa ne sannan zai yi nasara a zaben shekarar 2023.
Da yake hira a gidan Talabijin na Arise TV, Tanko yace Musulmi mataimaki da Tinubu zai dauka zai sa mutanen jihohin Arewa da yawa au zabeshi.
Bai wuce dai kwanaki 3 ba suka ragewa jam’iyyun siyasa su fitar da mataimakansu kamar yanda dokar hukumar zabe ta INEC ta tanada.
Karanta wannan Bidiyo: 'Yan Achaba a kasar Kamaru na zanga-zangar vire tallafin man fetur a Najeriya